BBC navigation

Hari akan wata majami'a a Nairobi ya yi sanadiyyar mutuwar yaro daya

An sabunta: 30 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 17:49 GMT
Hari kan majami'a a Nairobin

Yaro daya ya mutu bayan harin da aka kai kan wata mujami'a a Nairobi

Wani hari da aka kai da nakiya kan wani coci a Nairobi, babban birnin Kasar Kenya ya yi sanadiyar mutuwar wani yaro, ya kuma raunata wasu da dama.

Wani kakakin 'yan sanda ya ce wasu daga cikin mutanen sun ji rauni ne a lokacin da ake turmutsutsin tserewa daga cocin na Saint Polycarp

Bayan wannan hari, 'yan sanda sun tarwatsa wasu matasa wadanda su ka kai farmaki kan wani masallaci.

Babban jami'in 'yan sanda na birnin Nairobin ya ce, za a hukunta duk wanda aka kama yana kai harin ramuwar gayya.

Ana dora alhakin hare haren da ake kaiwa kan mujami'u a baya bayan nan kan kungiyar 'yan gwagwarmaya ta Al-Shabaab dake Somalia, inda aka tura dakarun Kenya, a wani bangare na rundunar dakarun tarayyar Afrika.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.