BBC navigation

Daruruwan 'yan Libiya sun mika makaman su

An sabunta: 30 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 05:18 GMT

Makamai a Libya

Daruruwan 'yan kasar Libya sun mika makamansu a wasu wuraren da aka tsara a Tripoli babban birnin kasar da birnin Benghazi na gabashin kasar.

Mika makaman ya biyo bayan wani kira da sojoji suka yi wanda aka yayata a gidan Talabijin.

Yawanci, sun mika kananan bindigogi ne, amma akwai wasu da suka mika makamai masu linzami da na harba rokoki, wasu ma sun mika tankokin yaki.

Sojojin sun ce sun yi mamakin irin yadda mutane suka amsa wannan kira.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.