BBC navigation

Amurka ta rasa sojin ta na 2000 a Afghanistan

An sabunta: 30 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 17:32 GMT
Sojan Amurka a Afghanistan

Ana ci gaba da kashe sojojin Amurka a Afghanistan

An kashe wa rundunar sojin Amurka, sojanta na dubu biyu a Afghanistan, a salon hare hare na baya bayan nan da fandararrun sojin Afghanistan kan kai.

An yi musayar wuta tsakanin dakarun Amurka da na Afghanistan a lokacin da lamarin ya auku a lardin Wardak, inda aka kashe wani dan kwangila, da kuma wasu dakarun Afghanistan su uku.

Ba a san takamaimai menene ya janyo musayar wutar tsakanin sojojin Amurka da kuma sojojin Afghanistan a wani wajen duba ababan hawa a lardin Wardak da yammacin jiyan ba

Komandan rundunar sojin Amurka a Afghanistan Janar John Allen ya fadawa kafar yada labaran Amurka ta CBS cewa ya fusata sosai game da yadda ake samun karuwar hare haren da sojin Afganistan suke kaiwa sojojinsa.

Rundunar tsaro ta kasa da kasa ta na kan bincike game da kisan

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.