BBC navigation

Rikicin manoma da makiyaya ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutane talatin

An sabunta: 17 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 20:29 GMT
Taswirar Nijeriya mai nunin Jihar Binuwai

Taswirar Nijeriya mai nunin Jihar Binuwai

Wata takaddamar kabilanci game da fili a Jihar Binuwai dake tsakiyar Najeriya wadda ta ki ci ta ki cinyewa ta haddasa wani harin da ya yi sanadiyar kisan mutane akalla 30 da kuma kuna gidaje.

Mai magana da yawun Gwamnan Jihar Binuwai, Cletus Akwanya ya ce fulani makiyaya sun kai hari a kan wata al'umar Tivi a ranakun lahadi da litinin.

Ya ce babu wanda aka kama sakamakon tashin hankalin a garin Yogbo mai makwabtaka da Jihar Nasarawa .

A lokuta daban daban dai tashin hankali kan faru a yankin tsakanin kabilun biyu, kuma dukanin kokarin da aka yi baya na kawo karshen shi ya ci tura.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.