BBC navigation

Kotu ta baiwa mata damar gadon gida a Botswana

An sabunta: 12 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 14:57 GMT
Matan Botswana

Matan Botswana sun samu nasara

Wata babbar kotu a Botswana ta yanke hukunci mai cike da tarihi cewar mata na iya gadon gida.

A baya dai dokoki na gargajiya sun baiwa maza ne kadai damar gadon gida, abinda ke nufin cewar matan za su rasa gidajen zama, idan har 'yan uwansu ko mazansu suka mutu.

Wakiliyar BBC ta ce, Alkalin kotun ya ce, dokar gargajiyar da ta haramtawa matan gadon gida, ba ta da wuri a al'ummar Kasar Botswana, inda tsarin mulki ya yi umurnin daidaito tsakanin maza da mata.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.