BBC navigation

'Yantakara sun fara mika takardunsu a Ghana

An sabunta: 17 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 20:56 GMT
Shugaba John Mahama

Shugaba John Mahama

'Yan takarar shugaban kasa da na 'yan majalisar dokokin kasar Ghana sun fara mika takardun neman tsayawarsu takara ga hukumar zabe ta kasar.

Sai dai daga cikin yan takara 13, biyu ne kawai suka mika takardun nasu a ranar farko.

Sun hada da Nana Akufo - Addo na babbar Jama'iyar adawa ta NPP da kuma Pakuis Ndu na Jama'iyar PPP.

Sai dai ana sa ran sauran za su mika na su gobe, ciki kuwa har da Shugaban kasa, John Mahama na Jama'iyar NDC da kuma uwargidan tsohon Shugaba JJ Rawlings,Nana Konadu Agyemang, ta jama'iyar NDP.

Aikin dai za a gama shi ne da karfe biyar na yammacin gobe.

A cikin watan Disamba mai zuwa ne dai za a gudanar da babban zabe na kasar ta Ghana.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.