BBC navigation

Mexico ta tabbatar da kashe wani madugun dillalan miyagun kwayoyi

An sabunta: 9 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 20:21 GMT
Shugaba Pena Nieto na Mexico

Shugaba Pena Nieto na Mexico

Hukumomi a Mexico sun tabbatar da cewar an kashe jagoran daya daga cikin kungiyoyin dillancin miyagun kwayoyi na Kasar, a lokaci guda kuma hukumomin sun tabbatar da cewar an sace gawarsa

Hukumomin sunce gwaje gwajen da akai a kan gawar ta- sa- sun tabbatar da cewar mutumin da aka kashe shine Heriberto Lazcano, wanda ya ke jagorantar kungiyar Zetas.

An dai yi gwaje- gwajen ne, jim kadan kafin a nemi gawar tasa a rasa

Wakilin BBC ya ce wasu rahotannin na cewa wasu 'yan bindiga ne suka kai hari a gidan da ake makokin sa, inda suka kwace gawar tasa da karfin tsiya

Sojin ruwan kasar sun ce ya mutu ne sakamakon wata musayar wuta da akai tare da sojin a arewacin Kasar.

Heriberto Lazcano dai na daya daga cikin mutanen da Mexico take nema ruwa a jallo, kuma har Amurka ma ta saka lada ta dala miliyan biyar ga duk wanda ya kamo shi.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.