BBC navigation

Gwamnati ta bayyana Kamfanonin da za su raba wuta a Najeriya

An sabunta: 17 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 15:49 GMT
Shugaba  Goodluck Jonathan da Mataimakinsa, Namadi Sambo

Shugaba Goodluck Jonathan da Mataimakinsa, Namadi Sambo

Gwamnatin Najeriya ta bayyana sunayen wasu kamfanoni goma da ta ce sune suka yi nasarar samun kwangilar rarraba wutar lantarki a wasu jihohin kasar.

Wannan dai wani bangare ne na shirin da take yi na bai wa 'yan kasuwa damar shiga a dama da su a harkar samar da wutar lantarki a kasar.

To sai dai ana zargin cewa an nuna son zuciya wajen zabar wasu daga cikin kamfanonin, sakamakon zargin da ake yi cewa suna da alaka da wasu jami'an gwamnatin kasar mai ci ko kuma wasu gwamnatocin da suka gabata.

Wasu daga cikin kamfanonin da ake zargin an baiwa fifiko a lamarin dai ana cewar na tsohon Shugaban kasar Janar Abdulsalami Abubakar ne da kuma na wasu na hannun daman Mataimakin Shugaban kasa, Namadi Sambo.

To amma Ministan wutar lantarki na kasar, Mr Darius Isyaku, ya musanta wannan zargi,ya na mai cewar babu wani son zuciya da aka nuna a zaben kamfanonin da aka yi a bayyanar jama'a.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.