BBC navigation

Rasha ta yi fushi da Turkiyya kan Syria

An sabunta: 11 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 16:09 GMT

Praministan Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan ya ce, jirgin saman Syrian da jiragen yaki na Turkiyya suka tilastawa sauka a birnin Ankara, ranar Laraba, na dauke ne da makamai da wasu kayan yaki da za a kai wa dakarun gwamnatin Syria.

Turkiyya ta ce, ta saukar da jirgin saman ne saboda tana zargin cewa, ana kokarin keta takunkumin da aka sa wa kasar ne.

Turkiyyar ta ce wasu rahotanni ta samu na asiri dake nuna cewa akwai makamai a jirgin saman.

Kampanin zirga zirgar jiragen saman kasar Syria ya musanta zargin cewa akwai makamai a jirgin.

Ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta ce tsayar da jirgin, wanda ya taso daga birnin Mosko, da jiragen yakin Turkiyya suka yi, ya jefa rayukan pasinjojin jirgin cikin hadari.

Bayan saukar da jirgin, fasinjoji da ma'aikatansa sun shafe sa'o'i suna jira,lokacin da ake gudanar da bincike a cikinsa.

An yi ta bincikeb wasu akwatuna da ake cewa kayan lantarki ne, kuma sai da aka kawo sojoji kafin su bari a binciki jirgin.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.