BBC navigation

Turkiya ta tilastawa Jirgin fasinjar Syria sauka a Ankara

An sabunta: 10 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 20:23 GMT
Ahmet Davutoglu, Ministan harkokin wajen Turkiya

Ahmet Davutoglu, Ministan harkokin wajen Turkiya

Gidan talabijin Turkiyar dai yace jiragen yakin kasar ne suka tilastwa jirgin fasinjar Syrian ya sauka a filin jirgin Ankara a Turkiyyar, don a bincike shi.

Ministan harkokin wajen Turkiyyar yace hukumomi na binciken jirgin.
Yace kasar sa shirye take ta hana shigar da makamai a Syriar.

Tunda farko dai gidan talebijin din yace ana zargin cewa jirgin, wanda ya taso daga Moscow, yana dauke da makamai ne.

Kasar ta Turkiyya dai na goyon bayan 'yan tawayen Syrian.

Kuma an samu matsalar harbe-harbe tsakanin kasashen biyu akan iyakarsu.

Babban kwamandan sojin Turkiyyar, Janar Necdet Ozel, yayi gargadin cewa kasarsa za ta dauki kaarin tsauraran matakai, idan Syria ta cigaba da harba rokoki cikin Turkiyyar.

Yace: "Kamar yadda ka sani, muna maida martani cikin gaggawa; kuma muna yi masu barna. Amma idan aka cigaba da harbo rokoki daga Syrian, zamu maida martani da karfi sosai".

Janar Ozel dai yayi wadannan kalaman ne a garin da wata rokar da Syrian ta harba ta kashe fararen hula biyar.

Wannan tilasta ma jirgin fasinjan Syrian ya sauka a birnin Ankaran shine mataki na baya-baya nan dake nuna kaarin tabarbarewa danganta tsakanin kasashen biyu.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.