BBC navigation

Uganda ta dakatar da biyan kudin Fansho

An sabunta: 12 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 19:50 GMT
Shugaba Yoweri Museveni na Uganda

Shugaba Yoweri Museveni na Uganda

Gwamantin Uganda ta dakatar da biyan kudaden fansho ga mutane fiye da dubu sittin, dalilin abinda ta kira matakin kawar da rashawa a tsarin biyan kudaden fanshon.

Wadanda lamarin ya shafa sun hada da tsoffin malamai da ma'aikatan gwamnati da sojoji.

Jami'ai sunce suna son ganin an daina biyan mutanen da suka kira su da ma'aikatan bogi, wadanda ke karbar kudaden fanshon da bayanai na karya, da kuma karbar kudaden fanshon mutanen da suka rigaya suka mutu.

Wakiliyar BBC ta ce shawarar dakatar da biyan kudaden Fanshon na zuwa ne bayan wani bincike da aka gudanar, ya gano cewar an biya dala miliyan 25 ga ma'aikatan fansho na boge su fiye da dubu daya a cikin Kasar.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.