BBC navigation

An sake kama tsohon ministan Ivory Coast

An sabunta: 1 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 21:30 GMT

'Yan sanda a Accra, Ghana, sun sake kama wani minista a tsohuwar gwamnatin Laurent Gbagbo ta kasar Ivory Coast.

'Yan sandan kasa-da-kasa, wato Interpol, ne suka sake kama Mr Justin Konen Katinan, kwanaki kadan bayan wata kotun majistre ta bada belin sa.

Lawyan tsohon ministan dai yace ba'a bayyana masa abinda yasa aka kama wanda yake karewar ba.

Da farko dai 'yan sandan Ghana ne suka kama shi bisa takardan sammacin da gwamnatin Ivory Coast ta mika masu.

Zargin 'yan gudun hijira

Da alamu dai kamun nasa ba zai rasa nasaba da zargin da gwamnatin Ivory Coast ta ke yi cewa 'yan gudun hijran kasarta dake zaune a Ghana na da hannu a harin da aka kai ma jami'an tsaronta a ranar 21 ga watan jiya ba.

A 'yan kwanakin da suka wuce ne dai gwamnatin Ivory Coast ta rufe kan iyakarta da Ghana bayan da tace wasu 'yan bindiga da suka kutsa kai cikin kasar daga Ghana sun kai hari a kan wasu jami'an tsaronta.

Sai dai rahotannin dake fitowa daga wajen sunce a jiya ne Ivory Coast din ta sake bude kan iyakar na-wucin-gadi don barin daruruwan jama'a dake zube a kan iyakar su sa mu su wuce.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.