BBC navigation

Dubban mutane sun yi zanga zanga a Port au Prince

An sabunta: 1 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 08:13 GMT

Masu zanga zanga a Haiti


Dubban mutane sun yi zanga-zanga a Port au Prince babban birnin kasar Haiti dan nuna rashin amincewa da Shugaba Michel Martelly.

Masu zanga-zangar sun dora wa Mr Martelly laifin hauhawar da aka samu ta farashin kayan abinci da cin hanci da rashawa.

Wasu sun rike jajayen katuna inda aka rubuta Mr Martelly ya tafka kura-kurai da dama tun bayan zabensa a bara, suka ce ya gaza cika duk wani alkawari da ya dauka a lokacin yakin neman zabe.

Alkawarurrukan sun hada da bayar da ilimi da muhallai kyauta bayan girgizar kasar da aka yi a shekara ta dubu biyu da goma.

Boren dai ya biyo bayan jerin zanga-zangar da aka shafe makonni ana yi ne a Kauyukan kasar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.