BBC navigation

Zaben Amurka 2012: Jihohin da za a fafata

An sabunta: 16 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 12:21 GMT

Yawancin Jihohi na da tarihin zaben wata jam'iyya a koda yaushe, kuma a yanzu ma dan takarar wadannan jam'iyyun na saran za su zabe shi. Hakan na nuna cewar jihohi kadan ne ba a san wanda za su zaba ba. Wadannan jihohin ne ake dauki ba dadi a kansu a lokacin zabe.

Ana zaben shugaban kasa ne ta hanyar amfani da wani tsari da ake kira Electoral College. Kowacce jiha na da yawan kuri'u bisa la'akari daidai yawan al'ummarta. Kenan wasu jihohi sun fi wasu yawan kuri'u.

Misali, California (na da yawan jama'a miliyon 37.7 tana da kuri'u 55, a yayinda jihohin dake kauyuka kamar Montana, tana da jama'a miliyon daya, kuri'unta uku ne. Dan takarar daya lashe zabe a jiha shi ne ke da duka yawan kuri'un da aka kada.*

Dan takara na bukatar kuri'u 270 ne don zamowa shugaban kasa.

Latsa nan don ganin wurare da jam'iyyu ke da rinjaye.

Jihohin da za ayi dauki ba dadi a kansu (Kuri'u 161). A wadannan jihohin babu dan takarar dake da alamun samun nasara kai tsaye. Jihohi masu launin algashi 'purple' a nan ne za a kashe kudaden kampe da lokaci don samun kuri'u.

Jihohin da jam'iyyar Republican ke da karfi (Kuri'u 191). Ana musu lakabi da jihohi masu launin ja 'red', kuma 'yan Republican su ne ake ganin za su samu galaba a cikinsu a yankin kudanci da kuma tsakiyar yammaci amma kuma suna kauyuka ne inda kur'iunsu basu da yawa.

Jihohin da 'yan Democrats ke da rinjaye (kuri'u 186) - An yi musu lakabi da jihohi masu launin shudi 'blue' na yankin arewa maso gabashi da kuma gabar yammacin kasar kuma galibinsu a birane suke a yayinda kuri'unsu ke da yawa.

Loading...

COLORADO, kuri'u 9

Colorado jiha ce da ke saman teku inda tsaunuka fiye da dubu daya cikinsu har da wadanda suka kai kafa 10, 000 ke kewaye da ita.

Kamar sauran jihohin yammaci wadanda ke da mafi rinjayen Hispaniyawa, a 'yan shekarun nan 'yan jihar Colorado sun koma jam'iyar Democrats duk da yake a shekarun baya sun goyi bayan jam'iyar Republican. Barack Obama dan jami'iyar Democrats ne ya lashe zaben da aka gudanar a shekarar 2008, bayan da sau uku a jere jam'iyar Republican tana lashe zaben jihar.

Sai dai har yanzu jami'yar Democrats ba za ta iya cewa ita ce ke da iko dungurungum da jihar ba idan aka yi la'akari da yadda jam'iyar Republican ta lashe zaben kujerun Majalisar Wakilai biyu daga jihar a shekarar 2010. 'Yan jam'iya ta uku mafi karfi ne suka hana jami'iyar Republican lashe zaben kujerar Majalisar Dattawa da ta gwamnan jihar. Masu kadawa jam'iyar Democrats kuri'a sun mayar da hankali ne a biranen Denver da Boulder, yayin da 'yan jam'iyar Republican suka mayar da hankali a yankunan karkara da kuma sabbin yankuna, inda masu tsattsauran ra'ayi suka fi yawa. Garuruwan da ke kewaye da birnin Denver za su kasance wuraren da za a fafata tsakanin jam'iyyu.

YAWAN JAMA'A

 • 70.0%FARARE
 • 3.8%BAKAKE
 • 20.7%SPANIC
 • 5.4%SAURAN JAMA'A

TATTALIN ARZIKI

 • $56,344 yawan kudaden shiga a kowacce shekara
 • 11.2% yanayin talauci
 • 8.20% yawan marasa aikin yi

YAYA SAKAMAKO YA KAYA A ZABEN KARSHE?

 • 8.4%
  A SHEKARAR 2000 REPUBLICAN CE TA YI NASARA
 • 4.7%
  A SHEKARA TA 2004 REPUBLICAN CE TA YI NASARA
 • 8.9%
  A SHEKARAR 2008 REPUBLICAN CE TA YI NASARA
previous next
Latsa jiha don ganin cikakken bayani a kanta

Jihohin da za a fafata

A wadannan jihohi kowanne dan takara zai iya samun nasara.Wadannan sune jihohin da za su fayyace sakamakon zaben.

Koma baya

COLORADO, kuri'u 9

Colorado jiha ce da ke saman teku inda tsaunuka fiye da dubu daya cikinsu har da wadanda suka kai kafa 10, 000 ke kewaye da ita.

Kamar sauran jihohin yammaci wadanda ke da mafi rinjayen Hispaniyawa, a 'yan shekarun nan 'yan jihar Colorado sun koma jam'iyar Democrats duk da yake a shekarun baya sun goyi bayan jam'iyar Republican. Barack Obama dan jami'iyar Democrats ne ya lashe zaben da aka gudanar a shekarar 2008, bayan da sau uku a jere jam'iyar Republican tana lashe zaben jihar.

Sai dai har yanzu jami'yar Democrats ba za ta iya cewa ita ce ke da iko dungurungum da jihar ba idan aka yi la'akari da yadda jam'iyar Republican ta lashe zaben kujerun Majalisar Wakilai biyu daga jihar a shekarar 2010. 'Yan jam'iya ta uku mafi karfi ne suka hana jami'iyar Republican lashe zaben kujerar Majalisar Dattawa da ta gwamnan jihar. Masu kadawa jam'iyar Democrats kuri'a sun mayar da hankali ne a biranen Denver da Boulder, yayin da 'yan jam'iyar Republican suka mayar da hankali a yankunan karkara da kuma sabbin yankuna, inda masu tsattsauran ra'ayi suka fi yawa. Garuruwan da ke kewaye da birnin Denver za su kasance wuraren da za a fafata tsakanin jam'iyyu.

YAWAN JAMA'A

 • 70.0%FARARE
 • 3.8%BAKAKE
 • 20.7%SPANIC
 • 5.4%SAURAN JAMA'A

TATTALIN ARZIKI

 • $56,344 yawan kudaden shiga a kowacce shekara
 • 11.2% yanayin talauci
 • 8.20% yawan marasa aikin yi

YAYA SAKAMAKO YA KAYA A ZABEN KARSHE?

 • 8.4%
  A SHEKARAR 2000 REPUBLICAN CE TA YI NASARA
 • 4.7%
  A SHEKARA TA 2004 REPUBLICAN CE TA YI NASARA
 • 8.9%
  A SHEKARAR 2008 REPUBLICAN CE TA YI NASARA

FLORIDA kuri'a 29

Ana yi wa jihar Florida lakabi da Sunshine State a turance, saboda tana da gabar teku inda 'yan yawon bude ido ke zuwa. Cikin gabobin tekun har da Disney World.

Babu wata jam'iya da za ta bugi kirjin cewa ita ce ke da gagarumin rinjaye a koda yaushe wajen lashe zaben jihar. Jihar ta kasance wacce ke raba gardama a zaben shugaban kasa tun daga shekarar 1996. A shekarar 2000, lokacin da fafatawa ta yi zafi tsakanin George W Bush da Al Gore inda suka yi kut da kut, lamarin da ya sa aka sake kidaya kuri'un da aka kada duk da yake Kotun Koli ta dakatar da ci gaba da sake kidaya kuri'un.

Jihar na da gamin gambiza; fararen fata 'yan darikar Protestant na zaune a arewacinta, yayin da Amurkawa 'yan asalin Cuba ke zaune a kudanci, kuma suna da ra'ayin jam'iyar Republican. Kazalika akwai wadanda ke zaune a maraya kamar Miami da Tampa; sai kuma yahudawa 'yan fansho da ke Palm Beach, da kuma 'yan kasar Cuba da ke magana da yaren Hispaniya wadanda 'yan Democrat ne. Batun 'yancin zama a Amurka dai shi ne kan gaba a wajen Hispaniyawa masu kada kuri'a, yayin da kiwon lafiya da batun kasar Israela ne ke gaba a wajen wadanda suka yi ritaya. Batun tattalin arziki dai shi ne ke kan gaba ga yawancin mutanen da za su kada kuri'unsu, a jihar da farashin gidajenta ya yi raga-raga.

YAWAN JAMA'A

 • 57.9%FARARE
 • 15.2%BAKAKE
 • 22.5%SPANIC
 • 4.3%SAURAN JAMA'A

TATTALIN ARZIKI

 • $47,051 yawan kudaden shiga a kowacce shekara
 • 13.1% yanayin talauci
 • 8.8% yawan marasa aikin yi

YAYA SAKAMAKO YA KAYA A ZABEN KARSHE?

 • 0.0%
  A SHEKARAR 2000 REPUBLICAN CE TA YI NASARA
 • 5.0%
  A SHEKARA TA 2004 REPUBLICAN CE TA YI NASARA
 • 2.8%
  A SHEKARAR 2008 REPUBLICAN CE TA YI NASARA

IOWA kuri'u 6

An samo sunan Iowa ne daga sunan mutane Ioway, Amurkawa 'yan kabilar India. An kuma yi wa jihar lakabi ne da jihar Hawkeye, don nuna girmamawa ga shugabansu mai suna Black Hawk.

Iowa ta yi fice ne saboda kasancewarta jiha ta farko da ke daukar nauyin tarukan masu ruwa da tsaki da ke zaben mutumin da zai yi wa jam'iya takarar shugabancin kasa. Jihar ta rabu biyu tsakanin 'yan jam'iyar Democrats da 'yan Republican a shekarar 2000 da 2004. Sai dai shugaba Barack Obama ya samu kuri'u mafi rinjaye a jihar a shekarar 2008.

Yammacin birnin da ke da kasar noma ya kasance wajen da ake noma hatsi, kuma jam'iyar Republicans na da magoya baya sosai a yankin. Ita kuwa jam'iyar Democrats tafi samun magoya baya a yankunan tsakiya da gabashin ciki har da babban birnin jihar, Des Moines da kuma garin da ke da babbar kwaleji, watau Iowa City. Jihar na da muhimmanci ta fannin noma inda ake kiwon aladu da kuma noman hatsi, lamarin da ya sanya bayar da tallafi a bangaren noma yake da muhimmanci a jihar.

YAWAN JAMA'A

 • 88.7%FARARE
 • 2.9%BAKAKE
 • 5.0%SPANIC
 • 3.5%SAURAN JAMA'A

TATTALIN ARZIKI

 • $48,457 yawan kudaden shiga a kowacce shekara
 • 12.4% yanayin talauci
 • 5.4% yawan marasa aikin yi

YAYA SAKAMAKO YA KAYA A ZABEN KARSHE?

 • 0.3%
  A SHEKARAR 2000 DEMOCRAT CE TA YI NASARA
 • 0.7%
  A SHEKARA TA 2004 REPUBLICAN CE TA YI NASARA
 • 9.5%
  A SHEKARAR 2008 REPUBLICAN CE TA YI NASARA

MICHIGAN ta samu kuri'u 16

Ana yi wa jihar Michigan lakabi da Great Lake State a turance saboda kamfanonin kera motar kasar na birnin Detroit da ke jihar.

Duk da cewa Jam'iyyar Democrat ce ke lashe zaben shugaban kasa a jihar tun shekarar 1992, George W Bush ya fadi zabe ne a jihar da rata 'yar kalilan a shekarar 2000 da 2004, kuma 'yan Republican na da tarihin samun nasara a zabukan jiha.

Ana yi wa Michigan lakabi da jihar da ta yi karkon kifi, a da ita ce cibiyar masana'antun kasar, sai dai a yanzu tana fama da mummunan rashin aikin yi tun lokacin da da aka fara samun koma baya a manyan masana'antu a shekarun 1980. Babban batun da zai ja hankali a yakin neman zabe a Michigan shi ne tattalin arziki, kuma musamman matakin da shugaba Obama ya dauka na samar da bashi ga biyu daga cikin manyan kamfanonin kera motoci uku na kasar a shekarar 2009 a lokacin da suke fuskantar tsiyacewa, matakin da 'yan jam'iyyar Republican da dama suka nuna adawa da shi, inda suka ce gwamnati na neman sanya baki ne a harkokin kamfanoni masu zaman kansu. 'Yan jam'iyyar Democrat sun ce basussukan sun taimaka wajen ceto kamfanonin, da kuma dubban guraben ayyukan yi.

YAWAN JAMA'A

 • 76.6%FARARE
 • 14.0%BAKAKE
 • 4.4%SPANIC
 • 4.9%SAURAN JAMA'A

TATTALIN ARZIKI

 • $47,461 yawan kudaden shiga a kowacce shekara
 • 14.1% yanayin talauci
 • 9.4% yawan marasa aikin yi

YAYA SAKAMAKO YA KAYA A ZABEN KARSHE?

 • 5.1%
  A SHEKARAR 2000 DEMOCRAT CE TA YI NASARA
 • 3.4%
  A SHEKARAR 2004 DEMOCRAT CE TA YI NASARA
 • 16.5%
  A SHEKARAR 2008 REPUBLICAN CE TA YI NASARA

MINNESOTA, Kuri'u 10

Tauraruwar arewa, shi ne taken jihar Minnesota, wannan yanki ne da al'ummarsa ke da alaka sosai da yankin Scandinavia wato kasashen Sweden da Norway.

Minesota tana da tarihin zabar jam'iyyar Democrat tun shekarar 1972, har a shekarar 1984, lokacin da duk sauran jihohi suka zabi Ronald Reagan. Sai dai George Bush ya fadi zabe a jihar ne da kuri'un da ba su taka kara sun karya ba a shekarun 2000 da 2004, kuma 'yan jam'iyyar Republican suna taka rawa a zabukan jiha inda suka lashe zaben gwamna a shekarar 2006, kuma sun kusa maimaita hakan banda kuri'u 10,000 a shekarar 2010.

Kamar sauran jihohin kasar, rashin aikin yi da batun tattalin arziki za su iya kasancewa muhimman batutuwa da za su ja hankali a yakin neman zabe a jihar Minnesota, musamman a biranen da ke da masana'antu irin su Minneapolis da St Paul da Duluth. Sai dai Minnesota ta saba daukar matsayin siyasa irin nata daban da sauran sassan kasar, kuma 'yan takarar jam'iyya ta uku na samun nasara a cikinta.

YAWAN JAMA'A

 • 83.1%FARARE
 • 5.1%BAKAKE
 • 4.7%SPANIC
 • 6.9%SAURAN JAMA'A

TATTALIN ARZIKI

 • $56,704 yawan kudaden shiga a kowacce shekara
 • 10.6% yanayin talauci
 • 5.9% yawan marasa aikin yi

YAYA SAKAMAKO YA KAYA A ZABEN KARSHE?

 • 2.4%
  A SHEKARAR 2000 DEMOCRAT CE TA YI NASARA
 • 3.5%
  A SHEKARAR 2004 DEMOCRAT CE TA YI NASARA
 • 10.2%
  A SHEKARAR 2008 REPUBLICAN CE TA YI NASARA

NEVADA, Kuri'a 6

Ana yi mata lakabi da jihar azurfa saboda dimbin arzikin wuraren hakar ma'adinin azurfa da take da shi. Muhimmin yanki a Nevada shi ne Las Vegas.

Nevada jiha ce da ta zabi dan takarar da ya yi nasara a zaben kasar tun shekarar 1980 i zuwa yanzu. Barack Obama ya lashe zaben da gagarumin rinjaye a jihar a shekarar 2008, kuma 'yan Democrat za su yi fatan ya maimaita samun irin wannan nasarar a shekarar 2012. Jihar tana da 'yan kabilar Hispaniyawa da yawansu ke dada karuwa, don haka batun 'yancin zama a Amurka na da matukar muhimmanci a yakin neman zabe a cikinta.

Rikicin tattalin arzikin shekarar 2008 ya shafi jihar Nevada sosai, rashin aikin yi ya tashin gwauron zabi zuwa kashi 15% a shekarar 2010, a don haka batun halin da tattalin arziki ke ciki zai taka muhimmiyar rawa a zabe a jihar. 'Yan Democrat na da rinjaye a biranen Las Vegas da Reno, yayinda Republicans ke da farin jini a unguwannin da ke kewayen Vegas da kuma suran sassan jihar, wadanda ke cike da gidajen gona da kuma cibiyoyin sojoji.

YAWAN JAMA'A

 • 54.1%FARARE
 • 7.7%BAKAKE
 • 26.5%SPANIC
 • 11.5%SAURAN JAMA'A

TATTALIN ARZIKI

 • $55,322 yawan kudaden shiga a kowacce shekara
 • 9.4% yanayin talauci
 • 12.1% yawan marasa aikin yi

YAYA SAKAMAKO YA KAYA A ZABEN KARSHE?

 • 3.5%
  A SHEKARAR 2000 REPUBLICAN CE TA YI NASARA
 • 2.6%
  A SHEKARA TA 2004 REPUBLICAN CE TA YI NASARA
 • 12.5%
  A SHEKARAR 2008 REPUBLICAN CE TA YI NASARA

NEW HAMPSHIRE, kuri'u 4

An yi mata lakabi da jihar Granite saboda yawan wuraren aikin gine-gine da ke cikinta.

New Hampshire jiha ce ta ka-zo-na-zo, kuma bisa mamaki tana da tarihin zabar jam'iyyar Republican a tsawon shekaru. Duk da cewa Barack Obama ya lashe jihar da gagarumin rinjaye, George W Bush ya lashe zabe a jihar a shekarar 2000, kuma a zaben rabin wa'adi na shekarar 2010, 'yan jam'iyyar ta Republican sun lashe zaben dan majalisar dattijai da kuma kujerun 'yan majalisar wakilai biyau na jihar. Idan Mitt rombey ya kasance dan takarar jam'iyyar Republican, kasancewarsa gwamnan makociyar jihar wato Massachusetts zai iya taimaka masa wajen sake ribato jihar ga jam'iyyar Republicans.

Jihar na alfaharin kasancewa ta farko da ke zaben fidda gwani da farko, kuma masu zabe a jihar suna son yin tambayoyi kai tsaye ga 'yan takarar shugabancin kasa a tarukan da sukan shirya a jihar. A lokuta da dama jihar na nuna adawa da ra'ayin gwamnati mai ci, kuma harajin ta mai sauki ya janyo mata 'yan kasuwa da suka yi fice da yawa da suke zaune a cikinta.

YAWAN JAMA'A

 • 92.3%FARARE
 • 1.0%BAKAKE
 • 2.8%SPANIC
 • 3.7%SAURAN JAMA'A

TATTALIN ARZIKI

 • $62,629 yawan kudaden shiga a kowacce shekara
 • 8.7% yanayin talauci
 • 5.7% yawan marasa aikin yi

YAYA SAKAMAKO YA KAYA A ZABEN KARSHE?

 • 1.3%
  A SHEKARAR 2000 REPUBLICAN CE TA YI NASARA
 • 1.4%
  A SHEKARAR 2004 DEMOCRAT CE TA YI NASARA
 • 9.6%
  A SHEKARAR 2008 REPUBLICAN CE TA YI NASARA

NEW MEXICO, kuri'a 5

Jihar New Mexico na da na da kashi na biyu mafi yawa na 'yan asalin Amurka.

New Mexico ta samu sakamakon zabe na kusa-kusa a shekarun 2000 da 2004 - Al Gore ya lashe jihar ne da kwarya-kwaryan rinjayen kuri'u 366 kacal a shekarar 200, yayinda a shekarar 2004, shugaba George Bush ya lashe jihar da rinjayen da bai taka kara ya karya ba na kuri'u 6,000. Sai dai Barack Obama ya lashe jihar da gagarumin rinjayen kashi 15% a shekarar 2008, sai dai duk da cewa 'yan Republican sun lashe zaben gwamna a shekarar 2010, binciken jin ra'ayin jama'a ya nuna cewa akwai yiwuwar jam'yyar Democrat ta sake rawar gani a shekarar 2012.

Jihar ta rabu ne bisa bangaren da mutane ke zaune, 'yan Democrat sun fi yawa a yankunan birane da ke arewacin, su kuma 'yan Republicans sun fi kwari a yankin kudu maso gabashi da ke da iyaka da Texas. 'Yan kabilar Latino sun sauya ra'ayi suka mara wa Barack Obama baya a shekarar 2008, kuma duk da cewaya gaza kawo wasu gagaruman sauye-sauye a tsarin 'yancin zama a Amurka, ra'ayin 'yan Republican kan batun bai samu karbuwa ba har yanzu ga mafi yawan 'yan Latino.

YAWAN JAMA'A

 • 40.5%FARARE
 • 1.7%BAKAKE
 • 46.3%SPANIC
 • 11.3%SAURAN JAMA'A

TATTALIN ARZIKI

 • $42,737 yawan kudaden shiga a kowacce shekara
 • 16.2% yanayin talauci
 • 6.5% yawan marasa aikin yi

YAYA SAKAMAKO YA KAYA A ZABEN KARSHE?

 • 0.1%
  A SHEKARAR 2000 DEMOCRAT CE TA YI NASARA
 • 0.8%
  A SHEKARA TA 2004 REPUBLICAN CE TA YI NASARA
 • 15.1%
  A SHEKARAR 2008 REPUBLICAN CE TA YI NASARA

NORTH CAROLINA, kuri'a 15

North Carolina ta yi fice kasancewar nan ne wurin da Orville da Wilbur Wright suka fara kirkiro na'ura mai tashi, kusa da Kitty Hawk a 1903.

North Carolina wuri ne da 'yan Republican suka mamaye tsawon shekaru da dama, amma Obama ya yi nasara da karamin rinjaye a 2008. Za a iya alakanta nasararsa da sauyin da jihar ta fuskanta a 'yan shekarun da suka gabata.

North Carolina na daya daga cikin jihohin da ke bunkasa cikin gaggawa a Kudancin Amurka. Ana samun kwararar daliban da suka kammala karatu zuwa cibiyoyin bincike da ke tsakiyar jihar. Baya ga karuwar 'yan kabilar Hispania da kuma bakake da suka dade a yankin, kuma wannan ya karawa jam'iyyar Democrats karfi a wurin.

YAWAN JAMA'A

 • 65.3%FARARE
 • 21.2%BAKAKE
 • 8.4%SPANIC
 • 5.0%SAURAN JAMA'A

TATTALIN ARZIKI

 • $45,131 yawan kudaden shiga a kowacce shekara
 • 15.1% yanayin talauci
 • 9.7% yawan marasa aikin yi

YAYA SAKAMAKO YA KAYA A ZABEN KARSHE?

 • 12.8%
  A SHEKARAR 2000 REPUBLICAN CE TA YI NASARA
 • 12.4%
  A SHEKARA TA 2004 REPUBLICAN CE TA YI NASARA
 • 0.3%
  A SHEKARAR 2008 REPUBLICAN CE TA YI NASARA

OHIO, kuri'a 18

Jihar da ta samar da shugabannin kasa bakwai a baya, sai dai mutumin da ya fi fice a jihar shi ne Thomas Edison.

Jama'ar Ohio basu taba goyon bayan dan takarar da bai yi nasara ba tun 1960, a don haka hankali zai kara karkata kan jihar a bana domin ganin ko Barack Obama zai rike 'yar karamar nasarar da yake da ita. 'Yan Republican na fatan dorawa kan nasarar da suka samu a zaben gwamna da Sanata a 2010.

Kamar jihohin da ke makwaftaka da ita na Michigan da Pennsylvania, a baya Ohio na sahun gaba wurin masana'antu, sai dai har yanzu akwai kamfanoni kamar Procter & Gamble da kuma Firestone Tires.Matsalar tattalin arzikin da aka yi fama da ita ta yi illa ga jihar abinda ya sa batun tattalin arziki yake kan gaba a zukatan masu kada kuri'a.

YAWAN JAMA'A

 • 81.1%FARARE
 • 12.0%BAKAKE
 • 3.1%SPANIC
 • 3.7%SAURAN JAMA'A

TATTALIN ARZIKI

 • $46,838 yawan kudaden shiga a kowacce shekara
 • 14.5% yanayin talauci
 • 7.2% yawan marasa aikin yi

YAYA SAKAMAKO YA KAYA A ZABEN KARSHE?

 • 3.5%
  A SHEKARAR 2000 REPUBLICAN CE TA YI NASARA
 • 2.1%
  A SHEKARA TA 2004 REPUBLICAN CE TA YI NASARA
 • 4.6%
  A SHEKARAR 2008 REPUBLICAN CE TA YI NASARA

PENNSYLVANIA, kuri'u 20

Jihar Pennsylvania jiha ce ta ake misali da ita wurin nuna 'yanci, ana kuma yiwa jihar lakabi da Keystone State.

Duk da cewa Pennsylvania ta goyi bayan Democrats a dukkan zaben shugaban kasa tun 1992, sun sha da kyar a 2000 da 2004. Sai dai nasarar da Republican suka samu a zaben gwamna da Sanata a shekara ta 2010, ta kara musu kwarin gwiwar lashe zaben shugaban kasa a bana.

Mai sharhi kan al'amuran siyasa na Democrats James Carville ya bayyana Pennsylvania a matsayin jiha mai matukar muhimmanci kamar "Philadelphia da Pittsburgh da kuma Alabama a tsakiya". Democrats ce ke samun nasara a yankunan masana'antu na Gabaci da Yammaci, yayin da Republican ke samun nasara a yankunan karkara. Matsalar tattalin arzikin da aka yi fama da ita ta yi illa ga jihar abinda ya sa batun tattalin arziki yake kan gaba a zukatan masu kada kuri'a.

YAWAN JAMA'A

 • 79.5%FARARE
 • 10.4%BAKAKE
 • 5.7%SPANIC
 • 4.2%SAURAN JAMA'A

TATTALIN ARZIKI

 • $50,028 yawan kudaden shiga a kowacce shekara
 • 13.2% yanayin talauci
 • 8.1% yawan marasa aikin yi

YAYA SAKAMAKO YA KAYA A ZABEN KARSHE?

 • 4.2%
  A SHEKARAR 2000 DEMOCRAT CE TA YI NASARA
 • 2.5%
  A SHEKARAR 2004 DEMOCRAT CE TA YI NASARA
 • 10.3%
  A SHEKARAR 2008 REPUBLICAN CE TA YI NASARA

VIRGINIA, kuri'u 13

Yawancin shugabannin Amurka na farko-farko sun fito ne daga Virginia, ciki harda Thomas Jefferson.

Kamar mafi yawan jihohin da ke kudancin Amurka, Democrats sun mamaye Virginia tun bayan yakin basasa har 1960 - lokacin da jama'ar jihar suka juya mata baya suka koma Republican.

Sai dai karuwar jama'a da kuma 'yan ci rani a 'yan shekarun nan ya karawa Democrats kwarin gwiwa. Musamman ganin yadda jihar ke da bakake da yawa. Barack Obama ya lashe zabe a nan a 2008 a karon farko da jam'iyyar Democrats ta yi hakan tun 1964, duka sanatocin jihar 'yan Democrats ne. Sai dai Republican sun kwace kujerar gwamna a 2009, kuma suna fatan hakan zai karfafa musu gwiwa a zaben shugaban kasa.

YAWAN JAMA'A

 • 64.8%FARARE
 • 19.0%BAKAKE
 • 7.9%SPANIC
 • 8.2%SAURAN JAMA'A

TATTALIN ARZIKI

 • $60,539 yawan kudaden shiga a kowacce shekara
 • 10.4% yanayin talauci
 • 5.9% yawan marasa aikin yi

YAYA SAKAMAKO YA KAYA A ZABEN KARSHE?

 • 8.0%
  A SHEKARAR 2000 REPUBLICAN CE TA YI NASARA
 • 8.2%
  A SHEKARA TA 2004 REPUBLICAN CE TA YI NASARA
 • 6.3%
  A SHEKARAR 2008 REPUBLICAN CE TA YI NASARA

WISCONSIN, kuri'u 10

Wisconsin ta yi suna sosai musamman saboda yadda aka tsara tutar jihar abinda ya sa ake mata lakabi da Badger State

Democrats sun lashe dukkan zaben shugaban kasa a nan tun daga 1988, sai dai da kyar suka sha a hannun Republican a 2000 da 2004. Republican sun kuma lashe zaben gwamna da sanata a 2010, don haka akwai kallo a zaben watan Nuwamba.

Barack Obama zai yi fatan ya ci gaba da rike rinjaye mai yawan da ya samu a zaben shekarar 2008, kuma zai samu taimako daga 'yan kungiyoyin kwadagon da ke da tasiri a jihar. 'Yan kwadagon na gaba-gaba wajen adawa da sabon gwamnan jihar dan jam'iyyar Republican Scott Walker wanda yake son hana 'yan kwadago hada kai wajen neman hakkokinsu. Wannan ra'ayi nasa ya janyo zanga-zangar da mutane da dama suka fito a cikinta aka kuma yi yunkurin yi wa gwamna Walker kiranye.

YAWAN JAMA'A

 • 83.3%FARARE
 • 6.2%BAKAKE
 • 5.9%SPANIC
 • 4.6%SAURAN JAMA'A

TATTALIN ARZIKI

 • $51,257 yawan kudaden shiga a kowacce shekara
 • 11,5% yanayin talauci
 • 7.5% yawan marasa aikin yi

YAYA SAKAMAKO YA KAYA A ZABEN KARSHE?

 • 0.2%
  A SHEKARAR 2000 DEMOCRAT CE TA YI NASARA
 • 0.4%
  A SHEKARAR 2004 DEMOCRAT CE TA YI NASARA
 • 13.9%
  A SHEKARAR 2008 REPUBLICAN CE TA YI NASARA

* In banda jihohin Nebraska da Maine, wadanda suke raba kuri'unsu bisa wanda ya yi nasara a mazabun 'yan majalisa da kuma sakamakon jiha baki daya.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.