BBC navigation

Amurka ta ce faduwar kudin Iran tasirin takunkumi ne

An sabunta: 2 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 06:14 GMT

Kudin Iran


Amurka ta ce faduwar darajar kudin Iran watau - rial - wata alama ce ta nuna tasirin takunkumin da aka garkamawa kasar saboda shirin ta na nukiliya.

Darajar kudin na rial ta fadi a kan dolar Amurka a ranar litinin, tun farkon wannan shekarar ta fadi da kimanin kashi tamanin bisa dari.

Sai dai kwararru sun yi kashedin cewa wani dalili da ya jawo faduwar darajar ta rial shi ne sakamakon bannar kudi da ake yi a cikin kasar ne ya haifar da ita.

Lokacin da yake magana a wani taro da ake yi a birnin New York, Ministan harkokin wajen Iran Ali Akbar Salehi ya sake nanata matsayin kasar Iran cewar ba makaman nukiliya take kerawa ba, yana mai cewa ba za a yafe wa kowacce kasa da ta yi amfani da su ba.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.