BBC navigation

Brazil ta jigbe sojoji a Rio de Janaeiro

An sabunta: 2 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 05:24 GMT

Shugaban kasar Brazil

Rundunar Sojin Brazil ta baza dubban sojojinta a wasu yankunan da talakawa ke zaune a Rio de Janeiro gabanin zaben kananan hukumomi da za a yi ranar lahadi.

Hukumomin sun ce sojojin za su tabbatar da an yi zaben cikin lumana a yankunan da ake hasashen za a yi tashin hankali.

Yankin na Rio de Janeiro wuri ne da dillalan miyagun kwayoyi da 'yan banga ke cin karensu babu babbaka.

Shugaban Kotun zabe na Rio de Janeiro ya ce an dauki matakai masu yawa don kare duk wata barazanar da za a yi wa masu kada kuri'a a ranar zaben.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.