BBC navigation

An fara shari'ar Henry Okah a Afrika ta Kudu

An sabunta: 2 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 10:17 GMT
'Yan kungiyar MEND a Niger Delta

'Yan kungiyar MEND a Niger Delta

An soma shari'ar tsohon shugaban 'yan gwagwarmayar Niger-Delta na Najeriya, a Afrika ta Kudu bisa zarginsa da hannu a bama-baman da suka tashi a Abuja a shekarar 2010.

Henry Okah ya musanta zarge-zarge 13 da ake masa, wadanda suke da nasaba da ayyukan ta'addanci.

A cewar kamfanin dillacin labarai na AFP, ministan Niger-Delta, Godsday Orubebe ya shaidawa zaman kotun na jiya cewa " Mr. Okah wani kusa ne na masu gwagwarmaya a yankin Niger Delta kuma 'yan gwagwarmayar na girmama shi."

An dai cafke shi ne a Johannesburg a washegarin tashin tagwayen bama-bamai da aka dasa a motoci a lokacin bikin cikar Najeriya shekaru 50 da samun 'yancin kai.

Hare-haren dai sun yi sanadiyyar mutuwar mutane 12 tare da jikkata wasu.

Kungiyar masu fafutuka ta yankin Niger Delta wato MEND ce ta yi ikirarin kai hare-haren.

An samu saukin kai hare-hare a yankin mai arzikin mai a Najeriya, tun bayan tayin afuwar da gwamnatin tarayya ta yi wa masu dauke da makamai a shekarar 2009.

Ana shari'ar Okah a Afrika ta Kudu ne bisa dokar kasar da ta bada hurumin yin hakan, saboda yana da shedar zama dan kasar.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.