BBC navigation

'Yan bindiga sun kashe ɗalibai a Mubi

An sabunta: 2 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 12:36 GMT

Rahotanni daga jihar Adamawa dake arewacin Najeriya na nuna cewa, sama da mutane 20 ne, mafi yawansu dalibai suka rasa rayukansu a wani harin da aka kai a makarantar kimiyya da fasaha ta Mubi.

Wasu 'yan bindiga ne suka kai harin a wajen kwanan dalibai dake wajen makarantar a daren jiya.

Rundunar 'yan sandar jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin, kodayake tace bata tantance yawan wadanda harin ya rutsa da su ba.

Wani dalibi ya shaidawa BBC cewa maharan, wadanda kawo yanzu ba a san ko su wanene ba, sun dinga kwankwasa kofar dakunan dalibai, inda suka dinga harbe su ko amfani da wuka wajen kashe su.

Al'amarin ya janyo zanga-zanga daga sauran daliban makarantar, abin da ya kai ga dage jarabawar da aka yi shirin farawa a yau.

A watan jiya dai mahukunta a Najeriyar sun ce sun cafke mutane 150 da ake zargin 'yan kungiyar nan ce ta Jama'atul Ahlul Sunna lil da'awati wal jihad, wacce aka fi sani da Boko Haram dake kai hare-hare a garin na Mubi.

Mutanen da jami'an tsaro suka ce suna cigaba da tsare su.

Kungiyar ta Boko Haram ta ce ta kai hari a kan turakun sadarwa a garin, abin da ya janyo wahalar sadarwa da mazauna garin na Mubi.

A makon jiya ne kuma jami'an 'yan sanda suka ce sun gano makamai da albarusai da dama a garin.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.