BBC navigation

Kamfanin China ya kai karar Obama

An sabunta: 3 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:08 GMT

Barack Obama

Wani kamfanin kasar China da ke gudanar da harkokinsa a Amurka ya kai karar Shugaba Obama saboda hana shi sayen wani filin noma da ke kusa da wani sansanin sojin ruwan Amurka a yankin Oregon.

Kamfanin mai suna Ralls Corporation ya ce gwamnatin Amurka ta zarta ikon da take da shi na hana kamfanin yunkurinsa na sayen filin noman saboda dalilan tsaro, ba tare da bayar da wata kwakkwarar hujja ba.

A cikin kundin karar da ta shigar, China ta zargi shugaban na Amurka da aikata abubuwan da suka sabawa doka.

Kazalika, China ta yi zargin cewa ba a yi wa kamfanin na China adalci ba kamar yadda doka ta tanadar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.