BBC navigation

Jami'an tsaro na bincike gida gida a Mubi

An sabunta: 3 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 15:59 GMT
Makarantar kimiyya da fasaha ta Mubi

Makarantar kimiyya da fasaha ta Mubi

Hukumomi a Najeriya na bin gida-gida suna bincike don gano musababbin abinda ya janyo kashe mutane akalla 26 a wani hari da aka kaiwa dalibai a wajen kwanansu a ranar Litinin a garin Mubi dake jihar Adamawa.

Kakakin gwamnatin jihar Adamawa, Mai Jama'a Adamu, ya shaidawa BBC cewar tashin hankalin na gari Mubi na da alamun cewar ya samo asali ne daga zaman tankiyar dake tsakanin dalibai, bayan zaben shugabanninsu da suka yi.

Hukumomi sun ce yawancin wadanda aka kashen sannannu ne wajen maharan.

Wasu mazauna garin na Mubi sun ce lamarin ya sa jama'a na barin garin zuwa wasu wurare.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.