BBC navigation

'Jami'an tsaron Sudan ta Kudu sun ci zarafin 'yan kasar'

An sabunta: 3 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:10 GMT
Amnesty International ta zargi jami'an tsaron Sudan ta Kudu da yin tabargaza

Tambarin Amnesty International

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International ta zargi jami'an tsaro a Sudan ta Kudu - wadanda aka dorawa alhakin kwace makamai daga hannayen mayaka a yankin gabashin kasar - da muzgunawa fararen hula, da kashe-kashe da kuma aikata fyade.

Gwamnatin kasar dai ta kaddamar da aikin dawo da zaman lafiya a farkon wannan shekara don takaita tashe-tashen hankula a tsakanin kabilu a jihar Jonglei, inda aka hallaka daruruwan mutane.

Sai dai maimakon magance rikicin, ana zargin sojoji da 'yan sandan kasar da aikata manyan laifuka da suka hada da rura wutar rikici.

Amnesty International ta ce ta gana da mutane da dama a gundunar Pibo, wadanda suka bayyana mata cewa an azabtar da mutane da yawa ciki har da yaran da ba su kai shekaru biyu a duniya ba.

Kalazila mutanen sun ce jami'an tsaron sun wawashe kayansu, sannan suka lalata musu amfani gona.

A baya gwamnatin Sudan ta Kudu ta yi kokarin ganin ba a fitar da irin wadannan rahotanni na cin zarafin bil adama ba.

Masu nazari na gani irin wadannan ayyukan keta hakkin bil adama na barazana ga kwarya-kwaryan zaman lafiyar da ake da shi a kasar, kana yana izar wutar kiyayya da gaba, da ma yiwuwar sake fadawa rikici.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.