BBC navigation

Ana ci gaba da gumurzu a Aleppo

An sabunta: 3 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 16:01 GMT
Aleppo na kasar Syria

Aleppo na kasar Syria

An kashe akalla mutane talatin da daya a yayinda wasu da dama suka samu raunuka, bayan fashewar wasu bamabamai a birnin Aleppo na Syria, a wani yanki da dakarun gwamnati keda iko.

Wasu motoci biyu makare da bamabamai ne suka tarwatse a dandalin dake tsakiyar birnin, ya kuma lalata manyan gine gine.

Yawancin wadanda suka gamu da ajalinsu dai fararen hula ne.

Ga abinda shugaban majalisar dokoki Syria, Jihad al-Laham yace game da harin.

A 'yan makwannin nan dai, birnin Aleppo ya kasance inda ake tafka kazamin fada tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawaye, inda aka raba birnin gida biyu.

A wani labarin kuma mutane uku sun mutu bayan da wani makamin roka da aka harbo daga Syria ya fada wani gida dake kan iyakar kasar da Turkiyya ta yamma maso gabashin kasar.

Wasu hotunan bidiyo da aka nuna a talbijin nun nuna hayaki da kura na tashi daga garin Akcakale dake kan iyakar kasashen biyu.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.