BBC navigation

Sarki Abdallah na Jordan ya rusa majalisar dokoki

An sabunta: 4 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 20:10 GMT
Sarki Abdullah na Jordan

'Yan adawa sun shirya gangami a Jordan ranar juma'a

A jajiberin wani babban gangami na 'yan adawa, Sarki Abdallah na Jordan ya rushe majalisar dokokin Kasar, tare da yin kiran gudanar da zabe

Sanarwar takaitacciya da aka fitar daga fadar Sarkin, bata bayyana ranar da za a gudanar da zabubbukan ba

Babbar jam'iyyar adawar Kasar ta The Islamic Action Front, ita ce dai ta kiran Zanga zangar da za a gudanar a ranar juma'a

Ana yi mata kallon ita ce kabulabale mafi girma ya zuwa yanzu ga Sarki Abdallan, tun lokacin da guguwar neman sauyi ta kada a yankin gabas ta tsakiya a bara

Tattalin arzikin Kasar mai rauni da cire tallafin mai, dama takaita hanyar sadarwa ta Intanet da kuma rikicin Kasar Syria dake makwabtaka, sune su ka rura wutar kiraye kirayen neman sauyi

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.