BBC navigation

"Za'a iya magance rikicin Mali da dabara". Inji Obasanjo

An sabunta: 4 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 20:16 GMT
Olusegun Obasanjo

Olusegun Obasanjo

An shirya a yau ne za a fara tattaunawa a Majalisar Dinkin Duniya kan shawarar da kasashen Yammacin Afrika suka bayar na tura sojoji zuwa Mali.

Rabin yankin Arewacin kasar ta Mali dai yana karkashin ikon masu tsaurin kishin Islama ne na kungiyar Ansar Dine, kuma kungiyar kasashen Yammacin Afruka ta ECOWAS ta gabatar da wani shiri na tura dakaru dubu uku zuwa yankin domin taimakawa a murkushe su.


A halin da ake ciki kuma 'yan kasar ta Mali da kansu suna cigaba da tattaunawa a kan makomar kasarsu a wani babban taro da ake yi a Bamako, babban birnin kasar.

Yanzu haka tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo na halartar wani taro da ake birnin Paris a kan kasar ta Mali, inda ya yi magana kan abi ta dabara domin warware matsalar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.