BBC navigation

Nijar ta fadakar da malamai kan zaman lafiya

An sabunta: 4 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 08:01 GMT

Shugaban Nijar, Mahamadou Issoufou

A jamhuriyar Nijar, Majalisar Koli ta addinin musulunci ta gudanar da taron karawa juna sani da ya hada wasu malaman da ke wa'azi a kasar.

An gudanar da taron ne don wayar da kawunan malaman ta yadda za su iya ba da tasu gudummawa ga kokarin da hukumomin kasar ke yi wajen tabbatar da kyakkyawar zamantakewa, da kuma rage kaifin ra'ayi a tsakanin al'ummomin kasar.

Mahalarta taron sun bayyana cewa akwai matukar bukatar nusar da 'yan kasar kan zaman lafiya saboda rikice-rikicen da makwabtansu ke fuskanta.

Hajiya Huda tana cikin malaman da suka halarci taron.

Ta shaidawa BBC cewa: '' Kur'ani ne ya koyar da mu zaman lafiya tun da fari. Manzon Allah (S.A.W) ya ce ya kamata musulmi su zama kamar jiki guda; idan yatsa guda ta ji ciwo ya kamata duk jiki ya amsa.Saboda haka manzon Allah shi ne babban misalin da ya kamata mu yi koyi da shi''.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.