BBC navigation

Kotu ta bada umurnin a mika Abu Hamza zuwa Amurka

An sabunta: 5 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 14:55 GMT
abu hamza

Abu Hamza, dan asalin kasar Masar ne

Wani ayarin motocin 'yan sanda ya bar wani gidan kurkukun Burtaniya zuwa wani sansanin Jiragen saman soji domin mika Malamin addinin musuluncin nan Abu Hamza da wasu mutane hudu da ake zargi,domin tura su zuwa Kasar Amurka don fuskantar wasu jerin tuhumar aikata ta'addanci.

Tun farko dai wata babbar kotu a London ta yanke hukuncin cewa a mika Malamin addinin Musuluncin mai tsauttsauran ra'ayi Abu Hamza ga hukumomin Amurka domin fuskantar tuhuma kan ayyukan ta'addanci.

Lauyoyin Abu Hamza sun gabatar da hujjar cewa yana fama da rashin lafiya, kuma akwai bukatar a binciki koshin lafiyarsa.

Akwai wasu mutanen hudu da suma aka yanke hukuncin cewa a mika su ga Amurkar.

Abu Hamza wanda aka haifa a kasar Masar, ana nemansa ruwa ajallo a Amurka akan tuhumarsa da kafa sansannin horadda 'yan ta'adda a Oregan.

Ana kuma zarginsa da hada baki wajen yin garkuwa da mutane a Yemen a shekarar 1998, a wani hadari daya janyo rasuwar mutane hudu.

Abu Hamza dai ya sha shekaru bakwai a gidan kaso a Birtaniya saboda tunzura jama'a.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.