BBC navigation

Dalibai 18 sun mutu sanadiyar ruftawar kasa a China

An sabunta: 5 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 08:09 GMT

Wajen da kasa ta rufta a China

Dalibai goma sha takwas ne suka rasu a lokacin da kasa ta rufta da wani ginin makarantar firamare da ke kudu maso yammacin China.

Kafofin watsa labaran kasar sun ce masu aikin ceto sun gano dukkan gawarwakin yaran a wani kauye da ke lardin Yunan.

Lamarin ya faru ne ranar Alhamis.

Duk da yake an yi hutun gama-gari ranar Alhamis a kasar amma yara sun je makarantun da ke kusa da gidajensu domin daukar darasi.

Sun yi hakan ne saboda cike gibin da ya faru sakamakon dakatar da karatu da aka yi saboda girgizar kasar da ta faru a yankin a watan jiya, wacce ta yi sanadiyar mutuwar mutane tamanin.

Batun kare rayukan jama'a shi ne a kan gaba a lamuran da ake tattaunawa a China.

Dubban dalibai ne suka rasa rayukansu lokacin da wata girgizar kasa ta yi kaca-kaca da wata makaranta a yankin Sichuan shekaru hudu da suka gabata.

Lamarin ya jawo zazzafar muhawara, inda aka zargi 'yan kwangilar da suka gina makarantar da yin gini mara inganci ganin cewa a lokacin da lamarin ya faru, wasu gine-gine da ke kusa da ita ba su fadi ba.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.