BBC navigation

Kotu ta yankewa 'yan gida daya su biyar hukuncin kisa

An sabunta: 5 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 15:04 GMT
india

Wata makwabciyar su Yogesh da Asha tana nuna gidan da aka kashe masoyan

Wata Kotu a Indiya ta yankewa wasu mutane 5 da suka fito daga gida daya hukuncin kisa, saboda samun su da laifin kashe wani saurayi da budurwar sa, shekaru biyu da suka gabata.

'Yan gidan su budurwar ne suka hallaka saurayin da budurwar, bayan sun yi adawa da dangantar su, saboda mutumin da yarinyar take so ya fito ne daga karamin gida na Hindu.

Masu fafutukar kare hakkin dan Adam a India sunce ana kashe daruruwan mutane a kowacce shekara saboda irin wannan dalili.

A bara dai kotun kolin kasar Indiyan ta bayyana cewar masu irin wannan kisan zasu fuskanci hukuncin kisa suma.

Shekaru biyu da suka gabata, Yogesh, wanda direban taxi ne, da Asha, 'ya a wajen wani mai sayar da kayan gwari, suka tsunduma cikin kogin soyayya inda har ma suke son su yi aure.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.