BBC navigation

Ta'addanci: An fitar da Abu Hamza daga Birtaniya

An sabunta: 6 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 05:50 GMT

Abu Hamza

An fitar da malamin addinin musuluncin nan Abu Hamza da wadansu mutane guda hudu daga Birtaniya zuwa Amurka don fuskantar zargin aikata laifukan ta'addanci.

Abu Hamza na fuskantar tuhumar aikata laifuka 11 wadanda suka hada da yin garkuwa da mutane, da hada baki domin kafa sansanin horar da 'yan ta'adda da makamantansu.

Za a gurfanar da shi a gaban kuliya cikin sa'oi ashirin da hudu.

Tuni alkalai a birnin Newyork ke jiran isowar Abu Hamza kasar.

Tun farko dai wata babbar kotu a London ta yanke hukuncin mika malamin addinin musuluncin ga hukumomin Amurka domin fuskantar tuhuma kan ayyukan ta'addanci.

Lauyoyin Abu Hamza sun gabatar da hujjar cewa yana fama da rashin lafiya, kuma akwai bukatar a binciki koshin lafiyarsa.

Abu Hamza, wanda aka haifa a kasar Masar, ana nemansa ruwa ajallo a Amurka akan tuhumarsa da kafa sansanin horar da 'yan ta'adda a Oregan.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.