BBC navigation

Ciwon sankarau ya barke a Amurka

An sabunta: 6 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 06:44 GMT

Kwayoyin cutar sankarau

Hukumomin lafiya na kasar Amurka sun ce kimanin mutane 47 ne suka kamu da wani nau'i na cutar sankarau wanda ake dangantawa da allurar gurbataccen sinadarin kara karfi da kiba.

Cibiyar kiyaye bazuwar cututtukan kasar ta ce mutane biyar ne suka rasu sakamakon cutar ta sankarau wacce ake kira fungal meningitis, wadda ba kamar sauran nau'i na cutar ba ba ta yaduwa daga wannan mutum zuwa wancan.

Ma'aikatan lafiya a kasar sun ce suna kokarin tuntubar dukkanin wadanda suka kamu da cutar a jihohin kasar 23 da suka yi allurar kara karfi da kiba, wadda yawanci ake yi wa masu fama da ciwon baya.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.