BBC navigation

Takunkumi: 'yan kasar Iran na dandana kudarsu, in ji Ban Ki-Moon

An sabunta: 6 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 06:06 GMT

Ban Ki-Moon da Ahmadinejad

Babban Magatakardar Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-Moon, ya ce 'yan kasar Iran na dandana kudarsu saboda takunkumin da kasashen duniya suka sanyawa kasar sakamakon yunkurin da take yi na kera makamin nukiliya.

Mista Ban ya bayyana hakan ne a cikin wani rahoto da aka gabatarwa babban taron Majalisar a watan Agusta, wanda sai a yanzu ne aka fitar da shi a bainar jama'a.

Ya ce matakan da Majalisar ta dauka a kan Iran- wadanda suka hada da takaita huldar da ake yi bankunanta - na yin mummunan tasiri kan rayuwar 'yan kasar.

Ya ce hakan ya kawo hauhawar farashi, da rashin ayyukan yi da kuma tsadar makamashi da kayayyakin masarufi.

Mista Ban kara da cewa takunkumin ya haifar da karancin abubuwan bukatu na yau da kullum musamman magunguna.

An dai gudanar da zanga-zanga a kasar Iran a farkon makon nan, saboda rage darajar kudin kasar, watau rial da gwamnati ta yi bayan da ya fadi a kan dala cikin makonni biyu.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.