BBC navigation

Najeriya: an kai hari a wata mashaya a Jalingo

An sabunta: 6 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 15:02 GMT

Rahotanni daga jihar Taraba sun ce kimanin mutane bakwai ne suka samu munanan raunuka, ciki har da kananan yara, bayan wani harin bom da aka kai a wata mashaya dake garin Jalingo a daren jiya.

Hukumar Agajin Gaggawa ta kasa a jihar NEMA, ta ce wannan shine harin bom na biyu cikin sa'oi ashirin da huɗu da ya auku a garin na Jalingo

Wadanda lamarin ya rutsa da su dai na kwance a asibiti ana yi musu magani.

Har yanzu dai babu wata kungiya da ta fito ta yi ikirarin kai wannna hari.

Cikin 'yan shekarun nan dai jihohin arewacin Najeriya na fama da hare-hare da ake dangantawa da ƙungiyar nan da ake kira Boko Haram.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.