BBC navigation

Kotu ta hukunta mai yiwa Paparoma hidima

An sabunta: 6 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 14:48 GMT

Paolo Gabriele, tsohon mai yiwa Paparoma hidima

Wato kotun birnin Vatican ta yankewa mai yiwa Paparoma hidima, Paolo Gabriele hukuncin zaman gidan kaso na shekaru uku ne, amma aka rage daurin zuwa na watanni goma sha takwas bisa hujjar cewa, a baya ba wata kotu da ta taɓa yanke masa hukunci saboda aikata wani laifi.

Paolo Gabriele wanda mai yiwa Paparoma Benedict hidima ne an yanke masa wannan hukunci ne saboda yin satar muhimman takardu na sirri a cikin gidan Paparoma.

Alkali Giuseppe Dalla Torre shi ne ya jagoranci zaman yanke hukuncin.

Yace, sun yankewa Paolo Gabriele hukuncin ne bayan samunsa da laifin da ya sabawa tanadin dokoki, da kuma cin amanar da aka danƙa a hannunsa.

Paolo Gabriele ya faɗawa kotu cewa, ya sace takardun ne kuma ya tsegunta su ga manema labarai saboda ya tona abinda ya ƙira, ayukan assha da yace, yana aikatawa a ƙololuwar cocin Roman Katolika.

Tsohon mai yiwa Paparoman hidima ya kuma ce, ya fallasa takardun sirrin na fadar Paparoma ne saboda ƙaunar da yake yiwa cocin na Roman Catholika.

Tun farko dai yayin zaman kotun Paolo Gabriele yace, shi a ganinsa bai aikata wani laifi ba.

Daga cikin takardun da aka samu a gidansa yayin bincike dai har wasu da ya ɗauke daga kan teburin Paparoma.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.