BBC navigation

A Amurka an gurfanar da Abu Hamza a gaban kotu

An sabunta: 7 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:09 GMT

Abu Hamza ya gurfana a gaban kotu

Babban malamin nan mai tsaurin kishin Islama Malam Abu Hamza wanda Britaniya ta kai Amurka don a gurfanar da shi gaban Kotu ya gurfana karon farko gaban Kotun a birnin New York.

Abu Hamza wanda ke fuskantar tuhumar da ta hada da hadin-baki a kafa sansanin horad da mayakan sa kai a Oregon da kuma hannu a satar wasu masu yawon bude ido a kasar Yemen zai kare kan sa a ranar talata.

Sauran wasu mutane hudun da aka kai can tare da shi sun bayyana cewar ba su da laifi.

Biyu daga cikin su suna fuskantar caji ne mai alaka da kai harin bam a ofisoshin jakadancin Amurka a kasashen Kenya da Tanzania a shekarar 1998.

Larry Numester na kamfanin dillancin labaran AP yana cikin Kotun a birnin Manhattan ya kuma gaya wa BBC Yace, "an zo da Abu Hamzan ne a Kotun ba tare da hannun sa na karfe ba."

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.