BBC navigation

Sojin Najeriya 'sun kashe 'yan gwagwarmaya'

An sabunta: 8 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 09:54 GMT
Sambo Dasuki

Yankin arewacin Najeriya na cigaba da fama da matsalolin tsaro

Rundunar tsaro ta hadin gwiwa wato JTF dake aiki a jihar Yobe dake arewacin Najeriya tace Sojin Najeriyar sun hallaka mutane 30 wadanda ake zargin 'yan Kungiyar nan da aka fi sani da suna Boko Haram ne, da su ka hada da masu kusanci da jagoran kungiyar, a wata musayar wuta da akai yau din nan.

Sanarwar JTF din ta kuma ce, an hallaka mutane 30 da ake zargin 'ya'yan kungiyar ne, bayan wata musayar wuta da aka dauki sa'oi da dama ana yi.

Sanarwar tace a musayar wutar an kashe wani babban Komanda a Damaturu da aka fi sani da Bakaka, wanda kuma ke kusanci sosai da jagoran kungiyar ta Boko Haram.

Rundunar ta JTF ta kuma ce ta kwace makamai da dama yayin samamen a garin Damaturu, babban birnin jihar Yobe.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.