BBC navigation

'Yan sandan Faransa sun kashe wani a farautar 'yan ta'adda

An sabunta: 7 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:19 GMT

Yan sandan faransa na samame

Yan Sanda a kasar Faransa sun harbe wani mutum har lahira a lokacin da suka kai wani samame na neman 'yan ta'adda a birnin Strasbourg.

An kuma kai irin wannan samamen a biranen Paris da Nice da Cannes inda aka kama Musulmi goma sha-daya masu kaifin kishin addini.

Wani mai gabatar da kara Franscois Molins ya bayyana cewar mutumin da aka kashe dillalin miyagun kwayoyi ne wanda ya rungumi addinin Musulunci yake tarayya da masu tsaurin kishin Musulincin.

Mai gabatar da karar ya ce a lokacin samamen, an kwace wata takarda da ta kunshi jerin sunayen wasu kungiyoyi na Yahudawa a sakamakon harin bam da aka kai a wani shagon sayar da kayan masarufi dake kusa da birnin Paris a cikin watan da ya wuce.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.