BBC navigation

An tilasatwa Fira Ministan Libya sauka daga mukamin sa

An sabunta: 7 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 20:11 GMT
Libya

Majalisar dokokin Libya ta yi fatali da batun kafa kwarya kwaryar gwamnati

An tilastawa Fira Ministan Kasar Libya sauka daga kan mukamin sa, bayan majalisar dokokin Kasar ta yi watsi da yunkurin sa na biyu kuma na karshe na ganin an kafa wata gwanati

Mr. Abu Shagur shine zababben Fira Ministan Libyan na farko, tun bayan da aka hanbarar da Marigayi Mu'ammar Gaddafi a bara.

Gidan talabijin din Kasar ya ce fiye da kashi 60 cikin 100 na 'yan majalisar basu da kwarin- gwiwar abubuwan da Fira Ministan ya gabatar masu

A yanzu dai majalisar dokokin Kasar zata zabi sabon Fira Minista cikin makoni uku zuwa hudu masu zuwa

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.