BBC navigation

A Tunisia an raunata 'yan sanda a wani bore

An sabunta: 7 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:38 GMT

Masu bore a Tunisia

Muhukuntan kasar Tunisia sun ce an raunata 'yan sanda masu dimbin yawa a lokacin wani bore a tsibirin Djerba da masu yawon bude ido ke ziyara don nuna rashin amincewa da sake bude wani wurin zubur da shara.

Wani kakakin gwamnatin ya ce masu zanga-zangar sun rinka jifa da duwatsu da bama-baman da aka yi na fetur tare da kai hari a kan wani caji ofis na 'yan sanda.

An barke da zanga-zangar ne a lokacin da 'yan sanda suka yi kokarin korar masu boren wadanda suka tare hanyar shiga wurin zubur da sharar.

Masu aiko da labarai sun ce a baya-bayan nan matsin rayuwa ya haddasa zanga-zanga da dama a wasu sauran sassa na kasar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.