BBC navigation

Kisan dalibai: 'Yan sanda a Rivers sun kama mutane 13

An sabunta: 8 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 12:47 GMT
'Yan sanda a Najeriya

'Yan sanda a Najeriya

Rundunar 'yan sanda a jihar Rivers dake kudancin Najeriya ta ce ta cafke wasu mutane 13 da take zargi da hannu wajen kisan wasu daliban jami'ar Patakwal hudu.

A ranar juma'ar da ta gabata ne aka kona daliban da ake zargin suna cikin kungiyoyin asiri.

Wasu gungun mutane ne suka kona laliban har lahira, bisa zarginsu da sace wayoyin salula na BlackBerry da kuma wasu kwamfitocin tafi da gidanka.

An aikata ta'asar ne a garin Aluu dake kusa da jami'ar Patakwal.

An sanya hoton bidiyon kisan daliban a shafin internate na You Tube.

Shugaban rundunar 'yan sandar Jihar Rivers, Ben Ugwuegbulam ya ce faifan bidiyon ne ya taimaka wa 'yan sanda kama wadanda ake zargi da hannu a lamarin.

Cikin wadanda aka kama, har da wani basaraken garin.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.