BBC navigation

Turkiyya ta mayar da martani ga Syria

An sabunta: 8 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 05:08 GMT

Rikicin Syria da Turkiyya


Sojojin kasar Turkiyya sun mayar da martani da manyan bindigogin artillery ga harin da Syria ta kai da wani makamin roka wanda ya fada kimanin mita dari biyu a cikin kasar ta Turkiyya.

Wannan shine lamari na baya-bayan nan a musayar wutar da kasashen biyu ke yi, kuma ya faru ne a kusa da wani Kauye na kan iyaka wurin da aka kashe mutane biyar a ranar Laraba.

Ba a dai ba da rahoton kisa ko jikkatar wasu mutane ba a wannan harin.

An tura sojojin Turkiyya su rinka sintiri a yankin kan iyakar kasashen biyu.

Prime Ministan Turkiyya Tayyip Erdogan ya ce kasar sa ta shirya shiga yaki idan hakan ya zama wajibi.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.