BBC navigation

An sake zabar Hugo Chavez shugaban kasa

An sabunta: 8 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 04:18 GMT

An sake zabar Hugo Chavez

An sake zaben Hugo Chavez a matsayin Shugaban kasar Venezuela.

Hukumar zaben kasar ta ce yayin da aka kidaya mafi rinjayen kuri'un da aka kada a zaben, Hugo Chavez ne ya lashe kashi hamsin da hudu bisa dari na kuri'un.

Mutane dai sun fito kwan-su da kwarkwatarsu a wurin zaben, wanda shine kalubale mafi girma na farko ga Mr Chavez da ya taba fuskanta tun lokacin da ya kama ragamar mulkin kasar a shekarar 1998.

A zaben sai da aka kara lokaci a wasu rumfunan zaben da aka samu dogwayen layuka.

An zabi Mr Chavez ne ya sake wani wa'adin mulki na tsawon shekaru shida inda zai cigaba da abinda ya kira juyin-juyi hali na 'yan gurguzu.

Kafin a ba da sanarwar sakamakon zaben babban abokin hamayyar sa Henrique Capriles ya bayyana cewar zai rungumi kaddara ko yaya zaben ya kaya.

Shi ma lokacin da ya kada kuri'arsa a wata Unguwar talakawa a birnin Caracas Shugaba Hugo Chavez ya bayyana cewar zai rungumi kaddara.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.