BBC navigation

Tarkacen tsunami na barazana ga Amurka

An sabunta: 9 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 09:52 GMT
Igiyar ruwan tsunami

Igiyar ruwan tsunami

Masana kimiyya a Amurka sun ce suna cikin matukar damuwa da barazanar da wasu kwayoyin halittu da tarkacen tsunami da ta shafi Japan ke yi.

Igiyar ruwa ce ke janyo kwayoyin halittun tare da tarkacen tsunami da ta shafi Japan a shekarar 2011.

Mafi rinjayen tarkacen har yanzu na cikin teku, amma akwai kimanin ton dari biyu da ya taru a wurin da jiragen ruwa ke tsayawa a Oregon dake gabar tekun pacific a Amurka.

Masana kimiyya daga Jami'ar jihar Oregon sun gano cewa, a matsayar jiragen ruwan akwai wasu kwayoyin halittu kimanin dari daya, wadanda babu irinsu a Amurka.

Guda uku daga cikin halittun da suka hada da tauraruwar ruwa da kaguwa ta gabar ruwan Japan da gamsakuka da ake amfani da ita wajen hada sabulu, an san suna barazana ga halittun dake yankin.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.