BBC navigation

Kamfanin Toyota ya yi kiranyen miliyoyin motocinsa

An sabunta: 10 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 15:37 GMT
toyota

Toyota Camry na daga cikin motocin da aka yiwa kiranye

Kamfanin kera motoci na Toyota ya ce zai sa a dawo da sama da motoci miliyan bakwai da dubu dari 4 daga duk fadin duniya.

Wadannan ne dai motoci mafi yawa da kamfani ya sa a dawo dasu a lokaci guda.

Kamfanin na Toyota ya ce abinda yasa ya nemi a dawo da motocin shi ne maatslar na'urar bude tagar motocin ne da ya gano, amma ya ce ba wata babbar matsla ba ce.

Sai dai kuma ta shafi samfurin motoci 11 da kamfanin ya kera daga shekara ta 2005 zuwa ta 2010.

Samfurin motocin Toyatar da abin ya shafa na daga cikin wadanda akafi sha'awa, don sun hada harda Yaris da Corolla da Camry da kuma RAV4.

Ta nemi a maido sune daga sassa dabam dabam na duniya, kuma kimanin motoci milyan biyu da dubu dari biyar ne abin ya shafa a Amurka, milyan biyu da dubu 800 kumaa Turai da China.

Kamfanin yace 'yan karamar matsala ce suke fama da ita, kuma za'a gyara ta a cikin kasa da awa daya.
Koda yake motocin da za'a maido din nada yawa, abin bai kai manyan matsalolin da kamfanin yayi fama dasu ba a shekara ta 2009.

A wancan lokacin an tilastawa kamfanin ya biya diyyar milyoyin daloli bayan da taki kiran a maido da motocin da suka samu matsalar totur.

Mutane da dama sun halaka a sabilin matsalar.

Tun daga lokacin kamfanin naToyota yayi kokari sosai don falfado da alkadarinsa.

A bana kasuwar motocinsa ta habaka a Amurka, ya kuma sake wuce kamfanin General Motors wajen zama kamfani mafi girma a kera motoci a duniya.

To saidai a China zanga-zangar nuna kyamar Japan ta shafi sayar da motocin Toyotar.

Cinikayyarsa ta fadi da kusan kashi hamsin bisa dari a watan Satumba, bayan da 'yan banga suka jawo wani mutun daga cikin motar Toyota a tsakiyar Chinan, suka yi masa mugun duka.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.