BBC navigation

Ko yaya Uganda za ta yi fama da rubanyar al'umma?

An sabunta: 10 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 17:30 GMT
Bikin samun 'yancin kan Uganda

Bikin samun 'yancin kan Uganda

A yayin da Uganda ta cika shekaru 50 da samun 'yancin kai daga turawan Ingila, ko yaya kasar za ta kasance nan da shekaru 50 masu zuwa a lokacin da yawan al'umar ta zai karu da ninki uku.

A dakin haihuwa na cibiyar kula da lafiya ta Kawempe da ke arewacin Kampala babban birnin kasar, ma'aikatan ungozoma biyu ne suke ta kai kawo.

Akwai dakunan haihuwa biyu a asibitin wadanda suka tsufa matuka, dakin kansa yana bukatar sabon fenti.

Dakunan na kunshe da gadaje da sauran kayan aiki, suma dai suna bukatar a sauya su.

''A wasu lokuta kana taimakon mai haihuwa, sai kuma wasu biyu su yanke jiki su fadi, su ma suna bukatar kulawar ka.'' In ji shugabar kula da bangaren haihuwa na cibiyar, Sara Kintu.

Ta kara da cewa ''a wasu lokutan ma minti 10 ne tsakanin kowacce haihuwa.''

Ta ce ''kana gamawa da mai haihuwa daya, ka gyara wajen sai kuma ka shigo da wata.''

Mutane bakwai a daki daya

Ga Naigaga Sinah, wannan shi ne karo na biyar da za ta haihu, ba ta wani sha wahala ba.

Ta iso cibiyar da safe tana nakuda, ta kuma haihu da rana, kana ta koma gida da yammaci.

"A yanzu haka ba na aiki, amma miji na yana aiki. Dan abin da yake samu da shi muke kula da yaran mu biyar."

Naigaga Sinah

Babu wani iface-iface ko hawaye, ta dai murtuke fuska tare da rike cikinta, kuma ba ta magana.

Haka al'amarin yake faruwa a fadin kasar.

Uganda na daga cikin kasashen da al'umarta ke habaka a fadin duniya, da kimanin kashi uku cikin dari a kowacce shekara.

Mace mai matsakaicin shekaru za ka same ta da 'ya'ya shida.

An yi kiyasin cewa nan da shekarar 2060, al'umar Uganda za su wuce adadin su na miliyan 32 a yanzu, zuwa fiye da miliyan 112.

Amma al'umar kasar na tunanin ta yaya za su iya da irin wannan yawan mutane.

Ga Mrs Sainah, damuwar ta ita ce yadda za ta kula da iyalinta.

Na ziyarce ta lokacin da ta koma gida, babu nisa daga cibiyar.

Gida ne mai ciki daya, da aka raba dakin da labule inda bangare daya aka mayar da shi falo dayan kuma dakin kwana.

Duk da kankantar sa, a gyare yake tsaf, an yi masa ado.

Wata mace da 'ya'yanta a Uganda

Wata mace da 'ya'yanta a Uganda

Ta karbeni cikin fara'a, da murmushi a fuskarta.

Ta dukufa yi wa yara wanka da hada musu abin karin kumallo, kai baka ce ba ta jima da haihuwa ba.

''A yanzu haka ba na aiki, amma miji na yana aiki. Dan abin da yake samu da shi muke kula da yaran mu 5.''

''Amma a yanzu ina so na dakata da haihuwa, sai na yi wa yara na tanadi. Idan rayuwa ta yi min dai-dai sai na kara haifar yara, watakila guda biyu''

''Ni da maigidana muna son samun babban iyali, idan muka ilmantar da su nan gaba idan sun girma za su kula da mu.'' In ji Mrs Sainah.

Uganda na da albarkatun kasa

Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni zai so al'ummar kasar ta habaka, dan hakan zai bunkasa arzikin kasar.

Hakan zai kara yawan ma'aikata, da kuma yawan mutanen da za su sayi kayayyaki.

Shugaban kasar da yake kan mulkin na tsawon shekaru 26, bai damu da yayi wa kasar tanadi don gaba ba.

A wata makala da ya gabatar a bikin cikar kasar shekara 50 da samun yancin kai, ya ce ''Girman kasar Burtaniya kamar Uganda yake, tana da yawan al'umma sama da miliyan 60 a yanzu. Kuma duk suna rayuwa mai kyau.''

Shugaban kasar Uganda, Yoweri Museveni

Shugaban kasar Uganda, Yoweri Museveni

"Kuma ba su da albarkatun kasa kamar Uganda. Kasar mu tana da tarin albarkatu fiye da kasashen da muke magana a kai.''

Domin cimma muradin shugaban kasar, gwamnatin kasar na bukatar ta kara ababen more rayuwa, kamar bangaren lafiya da ilimi.

Kuma yana da kyau gwamnati ta tabbatar tattalin arzikinta zai samar da ayyukan yi ga al'umar da take tasowa nan gaba.

Sai dai masu sharhi akan al'amuran gwamnati sun ce, bangaren lafiyar kasar na cike da matsaloli, haka batun yake a bangaren ilimi wanda ba ya taka rawar a zo a gani wajen samar da nagartaccen ilimi ga dalibai, kana babu ababen more rayuwa kamar wutar lantarki da hanyoyi da hanyoyi masu inganci.

Ingantacciyar rayuwa

Gamayyar jam'iyyun adawa na 4GC sun fara zanga-zangar wayarwa da al'uma kai akan rashin cigaban kasar.

Sun gudanar da zanga-zangar neman 'yancin kai.

Shugabannin jam'iyyun adawa da dama aka kama a dan tsakanin nan, saboda kokarin da suka yi na shiga tsakiyar birnin Kampala.

Lamarin da ya sa sai da 'yan sanda suka harba barkonon tsohuwa, domin tarwatsa jama'ar da suka kewaye babban dan adawar Kizza Besigye.

Mr Besigye yace gwamnatin da bata iya kula da mutanen kasar miliyan 35 ba, ta yaya za ta kula da adaddin da ya rubanya hakan sau uku?

Karin kudaden shiga daga man Petur

Gwamnatin Uganda tana shirin mayar da kasar ta zama cikin jerin kasashen da suke samun matsaikacin kudin shiga daga nan zuwa shekarar 2040.

Shugaba Museveni ya kuma ce yana fatan Uganda za ta zamo kasa ta farko a duniya nan da shekaru hamsin masu zuwa.

Al'umar kasar Uganda

Al'umar kasar Uganda

Duk da ana bikin cikar kasar shekaru 50 da samun 'yancin kai, amma al'umar kasar na ganin cewa kamata ya yi a ce kasar ta fi hakan cigaba.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.