BBC navigation

'Yan sandan Birtaniya sun zargi mutane biyu da laifin ta'addanci a Syria

An sabunta: 10 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:34 GMT

'Yan sandan Birtaniya

'Yan Sandan Britaniya sun ce sun kame wasu mutane biyu a filin jirgin saman Heathrow kan binciken da suke yi na tallafi ga Syria.

Birtaniyar na zargin su da tafiya zuwa kasar Syria don tallafa wa ayyukan da ake zargin na ta'addanci ne.

An tsare wani Namiji da Mace bayan sun sauka a filin jirgin saman da yammacin ranar Talata.

Jami'an 'yan sanda na binciken wasu gidaje biyu dake gabashin London a wani bangare na binciken.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.