BBC navigation

Ba Amurke ya mutu bayan lashe gasar cin kyankyasai

An sabunta: 11 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 10:47 GMT
Kyankyaso

Kyankyaso

Wani mutum wanda ya lashe wata gasa ta cin kyankyasai ya mutu, jim kadan bayan ya hadiye su da rai tare da tana a Florida, a cewar hukumomi.

Edward Archbold mai shekaru 32 ya kamu da rashin lafiya, ya kuma yanke jiki ya fadi a shagon sayar da dabbobi, inda aka yi gasar dake birnin Deerfield Beach, a ranar Juma'ar da ta gabata.

Kimanin mutane 30 ne suka shiga gasar da aka yi a shagon Ben Siegel.

Mahukunta dai na jiran sakamakon gwajin da aka yi wa gawar Mr. Archbold don gano musabbabin mutuwarsa.

Sai dai babu daya daga cikin sauran abokan gasar tasa da ya kamu da rashin lafiya, a cewar ofishin 'yan sanda.

"Sam ba mu ji dadin lamarin ba," Inji mai shagon, Ben Siegel.

Inda ya kara da cewa "Mutumin yana da haba-haba kuma kamar ya so ya nuna burge wa ne"

Ya kuma bayyana cewa Mr. Archbold bai nuna alamun rashin lafiya ba kafin fara gasar.

Lauyan mai shagon ya ce, duka wadanda suka shiga gasar, sun rattaba hannu a kan wata takarda, inda a cikinta suka amince da cewa sun dauki alhakin duk wani abu dangane da wannan gasar da ba a saba yin irinta ba.

Kyautar mesa aka ce za a baiwa wanda ya lashe gasar, kuma Mr. Archbold ya yi niyyar sayar da mesar ga wani abokinsa wanda ya kai shi wajen gasar.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.