BBC navigation

Brahimi na ziyara a Turkiyya

An sabunta: 13 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 15:07 GMT

Lakhdar Brahimi, mai shiga tsakani a rikicin Syria

Yayin da zaman ɗar-ɗar ke ƙaruwa tsakanin Turkyiyya da Syria, mai shiga tsakani a rikicin Syrian amadadin majalisar ɗinkin duniya da ƙungiyar ƙasashen larabawa, Lakhdar Brahimi zai je birnin Santanbul domin yin wata ganawa.

Cikin 'yan makonnin nan dai an fuskanci sa-in-sa akan iyakar Turkiyya da Syria, inda har aka kashe mutum biyar sakamakon wani harin da aka kai daga Syria zuwa wani ƙauyen Turkiyya.

Wakilin BBC yace, mai shiga tsakanin na musamman yana ƙoƙarin lalubo hanyoyin kawo ƙarshen tashin hankalin dake faruwa a Syria, kuma ya je Turkiyya ne domin ƙasar tana taka rawa sosai a rikicin na Syria.

Har ya zuwa yanzu dai Lakhdar Brahimi ba shi da wani taƙamaimen tsarin wanzar da zaman lafiya a Syria.

Rikici tsakanin Syria da Turkiyya dai na cigaba da ƙaruwa.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.