BBC navigation

Miliyoyin mutane na fuskantar cin zarafi a China- Amnesty

An sabunta: 11 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:53 GMT
Mutun mutumin wani mai ilmin falsafa a kasar China

Mutun mutumin wani mai ilmin falsafa a kasar China

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International, ta ce miliyoyin mutane ne ke kara fuskantar cin zarafi sakamakon amfani da karfin tuwo da ake yi wurin fitar da su daga muhallansu.

Amnesty ta ce, hukumomin yankunan kasar na kwace gidajen al'umma ta siyar ga dillalai, wadanda ke gina gidajen da suka fi karfin al'ummar dake yankin, domin samun kudaden shiga sakamakon dinbin basussukan da take fuskanta.

Kungiyar ta Amnesty ta ce, jami'an kananan hukumi na gallazawa tare da tilastawa jama'a barin muhallinsu, ko kuma su kwace musu filaye, a wasu lokutan ma su rushe gidajen jama'a.

Babbar daraktar kula da bincike ta Kungiyar ta Amnesty a Hong Kong, Nicola Duckworth ta shaidawa BBC cewa, gwamnatin kasar Chinar na yi wa jami'an kananan hukumomin karin girma ne idan har suka gina hanyoyi, masana'antu, da gidaje, amma kuma tana dan bincika wadanda suka kwace filaye ta karfin tuwo daga hannun masu shi.

Ta ce Kananan hukumomin sun ciwo basussuka masu yawa domin gudanar da ayyukna gine-gine, wanda yanzu kuma suke bukatar biya, amma kuma ta hanyar kwace wa tare da sayar da filayen jama'ar ga wasu dillalai.

Binciken da kungiyar ta Amnsety ta gano ta ce abu mai tada hankali shi ne, kwace gidajen mutane tare da cuzguna musu na sanya wasu su kashe kansu da kansu.

Kungiyar ta Amnesty ta ce ta samu rahotannin mutane 41 da suka hallaka kansu tsakanin shekarun 2009 zuwa 2012.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.