BBC navigation

Tattalin arzikin duniya na fuskantar barazana - IMF

An sabunta: 11 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:42 GMT
Taron Hukumar bayar da Lamuni ta Duniya IMF

Taron Hukumar bayar da Lamuni ta Duniya IMF a birnin Tokyo

Shugabar Asusun bayar da Lamuni ta duniya IMF, Christine Lagarde, ta ce farfadowar tattalin arzikin duniya na fuskantar barazana, saboda gwamnatoci ba sa daukar matakai cikin sauri, don gudanar da sauye-sauyen tattalin arzikin da suka dace.

Miss Lagarde ta bayyana cewa matsalar tattalin arzikin Nahiyar Turai da banbance-banbance game da yadda za a shawo kan matsalar shi ne ya fi yin barazana ga tattalin arzikin.

Sakon Ms Lagarde ga shugabannin kasashen duniya dai mai zafi ne, inda ta yi suka ga shugabannin Amurka, tana mai cewa rashin samun matsaya kan yadda za a fuskanci yanayin basussukan da suka addabi Amurkar na tsoratar da masu zuba jari, wanda ke nuna cewa farfadowar tattalin arzikin duniya na fuskantar barazana saboda siyasa.

Shugabar ta IMF dai ta ce akwai abubuwa da dama da ke haifar da matsalar, wanda kuma babban abin damuwa ne da ke da sarkakiya wajen yin sharhi a kai, ko kuma a dakilewa matsalar cikin sauri.

Inda ta ce akwai yanayi na rashin tabbas dake hana masu ruwa da tsaki kan harkoin tattalin arziki zuba jari, da ma samar da ayyukan yi.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.