BBC navigation

Jama'a a Mali na neman a kai musu dauki

An sabunta: 11 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 20:13 GMT
Masu zanga-zanga a Bamako

Masu zanga-zanga a Bamako

Jama'a a Bamako babban birnin kasar Mali sun gudanar da wata zanga zanga a yau, su na neman kungiyar raya tattalin arzukin Afurka, ECOWAS ko CEDEAO da ta dau matakin gaggawa na tura sojoji arewacin kasar.

Kungiyar masu kaifin kishin Islama ta Ansaruddeen dai ta kwace iko da arewacin kasar ne bayan juyin mulkin da akai a farkon wannan shekarar.

Masu zanga-zangar dai sun yi ta daga kwalaye dake dauke da rubuce-rubucen dake yin Allah-wadai da dakarun masu kaifin kishin Islama da suka kwace iko da arewacin kasar Mali bayan juyin mulkin da aka yi.

Kungiyar ECOWAS dai tayi alkawarin aike rundunar soja mai dakaru dubu uku zuwa arewacin Mali, idan har suka samu goyon bayan kasashen duniya.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.